Gaskiya Dokin Karfe

Galadima.com.ng Domin sharhi kan al amuran yau da kullum

Matakai 8 Da Mai Karamar Sana'a Zai Bunkasa Kasuwancunsa

Matakai Guda Takwas (8) Da Mai Karamar Sana’a Zai Bunkasa Sana’arsa
Dan uwa da ‘yar uwa yau ina son na baku wasu ‘yan shawarwari musamman ga ‘yan uwa na masu kananan sana’o’i wanda Insha Allahu idan muka rike su to saura kiris muma a fara kiranmu
Dangote
Eh mana ko kai baka so sana’ar ka ta bunkasa? Kaima kayi katon gida kayi mota ka taimakawa ‘yan uwanka, ka tallafawa marayu kamar
Jarman Sokoto
Idan kabi wannan matakan to Insha Allahu idan a rana mutum biyar suna siyan kayanka yanzu zasu koma mutum goma koma sama da haka.
Abokina kai da kake karamar sana’a ba wai Allah ya rubuta maka cewa akanta zaka dauwama ba, yadda in ka mutu shima danka ya gajeka akanta ba.
Kafin in kawo matakai
Zaka samu magidanci yana yaron shago a kantin kwari, shi da mai shagon ba zaka iya rarrabe waye ya girmi wani ba, suna da ‘Ya’ya sai mai shago ya biyawa dansa kudin makaranta kai kuma yaron shago kana faman ya baka ka samu na kaiwa bakin salati, don haka da danka ya gama Secondary School maimakon ya cigaba da makaranta sai kaje ka roki mai shago cewa danka zai fara zuwa haka zaku cigaba da rayuwa, sai bayan shekaru uku (3) dan mai shago yazo da Degree ya dinga juya ‘Da da Mahaifi, wato dai ku a haka kuke son ku karar da rayuwarku!
Dan uwana ‘Dan Mai Karas da Dan Mai Yalo wannan hanyoyin da zan kawo idan ka bisu to babu shakka idan ka taso gidanku ana cin Wake da Shinkafa & Mai da Yaji to yanzu lokaci yayi da zaka canja kana cin irin abincin da su Baba Buhari keci. (ka san shinkafar da talaka ke kukan tayi tsada ba irinta ake ci a Abuja ba?).
Kar na cikaku da surutu ga jerin matakan da yakamata ka bi:-
1. Ingancin Kayanka:- dole ka tabbatar da ingancin kayanka cewa ko ina aka zaga za’a gamsu cewa babu Ojoro babu almundahana acikin kayanka.
2. Dalilin da Yasa Mutum Zai Sayi Kayanka: dole ne ka samar da dalilin da zai gamsar da mai sayen kayanka, misali ina siyar da Rigar Sanyi to dole in yi maka bayanin rigar da irin alfanunta wanda Idan har ka gamsu to kai da kanka zaka kara kawo min sabbin masu siya (costumer).
3. Ka tsara ka suwancinka misali in tsara cewa a kullum ina son na siyar da kaya guda kaza, don haka a wata guda ina siyar da kaya guda kaza, sai na rubuta to in an samu kari ko ragi zan dinga ganewa, sabanin yadda mafi yawanmu keyi, kawai na siyo ya kare na kuma siyowa na zari kaza aciki shikenan.
4. Dai-daita Farashi a nan kada ka zama mai tsauwalawa jama’a domin zaka kore costumer dinka, haka kuma kada kayi sauki da yawa yadda ba zaka dinga cin ribar azo a gani ba, kada kazo kana yin sana’a amman ba zaka iya biyan kananun bukatunka ba.

Abubuwa Ga Wanda Zai Fara Kas
1. Ka dinga rubuta duk bayananka na kudi abinda ya shigo da abinda ya fita, ko Biscuit ka siya da kudin ciniki ka dinga rubutawa.
2. Ka nemo masu siya, a nan akwai nau’ikan masu sana’a guda biyu kamar haka”-
a. Wanda yake siyar da kayan amfani na yau da kullum.
b. Wanda yake siyar da kayan da in aka siya sai kuma bayan wani lokaci za’a kara siya.
Dukkansu mutum yake yakamata yayi nazari ya kuma yi amfani da salo iri-iri a kuma ko ina ya tallata sana’arsa, kwanaki naje wani taro a nan Kano da wani kamfani daga kasar Phylipis suka shirya a wajen taron wani yake bada misalin yadda ya fara neman customer daga suna hira a majalisa ya bada labari, sannan naje wasu yanki na kudancin Nigeria na gani mai sana’a baya jin kunyar tallata sana’arsa a ko ina, mu kuma a nan Mata ne suke da wannan kwarewar, kada kaje kunyar kowa kace “Ya Alhaj ina siyar da kaza fa idan kuna so” duk sanda ka shiga Sharfadi.com na san kuna ganin Do You Need a Website? nima tallana ne idan kaji mai so sai ka tambayeni.
Kayi amfani da social media domin tallata sana’arka domin samun costumers.
3. Ka dinga lissafa ribar da ka samu lokaci zuwa lokaci, idan har kana rubuta komai kuma zaka lissafa to zakaga ba karamar riba kake samu ba, rashin hakan ne yasa kullum ka cewa Bahaushe yaya kasuwa sai yace maka “to Alhamdulillahi” ka suwa sai a hankali har yau an kasa samun yaushe kasuwar zatayi hankali!
4. Mu dinga godewa Allah Idan har muka bi wadannan tsaruka to sai mu godewa Allah domin a Alkur’ani Allah da kansa ya tabbatar mana cewa idan har mun gode masa to zai kara mana.