Gaskiya Dokin Karfe

Galadima.com.ng Domin sharhi kan al amuran yau da kullum

TSEGUMI 10

TSEGUMI-10
.
"Sai ina kuma?"Na tambayi kaina a lokacinda na shigo mota. Gida ya kamata na koma 'dauko takardar da na samo a kamfanin takalma na Jogana domin bibiyar sauran mutanen da ban samu damar zuwa wajensu ba gameda Abubakar. Cinkoso da gosulon motocine ya dakatar dani a hanya,le'kawar da zanyi ta mirrow na hangi blue peugeot 'dinnan a bayana motoci uku a tsakaninmu. "Yau kam sai naga wanda ke bibiyata"nace a raina lokacinda na fito daga motar na tunkari blue peugeot d'in. Ban 'karasa isa ba mutumin da ke ciki ya bud'e 'kofar da gaggawa ya tsallake gefen titi sama ko 'kasa na nemeshi na rasa. Sai da na 'karasa har cikin motar cusa kan da zanyi ne wani dadda'dan 'kamshi ya daki hancina. Babu komai a motar sai wani 'dan 'karamin agogon hannu na mata a ciki. "Me kuma ya had'a namiji da agogon mata?"Na tambayi kaina.
Ban sha wahala ba wajen iske gidan mutumin da naga sunansa da adreshinsa a jikin takardar ba a unguwar Nasarawa yake.
"Malam barka dai"nace dashi bayan mun gaisa
"Yauwa"
"Don Allah ina tambayar wani abokinka ne Abubakar Garba"
"Waye kai?"
"Sunana Haidar"
"Taya akai kasan abokina ne?"
"Nasan hakane a kamfanin takalma na jogana kasancewar kan zuwa wajensa kuna gaisawa"
"Ok ! Gaskiya rabona Abubakar tun yana aikin kwandasta(karenmota) shekaru uku da suka wuce ban sake ganinsa ba"
"Kana nufin yana zuwa nan shekaru uku da suka wuce?"
"Eh"
"Amma a lokacin a ina yake da zama?"
"Tsamiyar boka nesa kad'an da police station"
"Amma direban da yakewa karen motar fa ka sanshi?"
"A'a ban sanshi ba gaskiy"
"Amma ka ta'ba ganinsa da wata yarinya ko ka ta'ba jin sunan Hadiza Abdullahi Adamri a bakinsa?"
"Eh to ina ganinsa da 'yan mata dai kam amma bansan wacece Hadizan ba cikinsu"
"Kace shekaru uku da suka wuce kuka daina had'uwa?"
"Eh amma akwai lokacin da na ta'ba ganinsa a gidan polo,yake fad'amin cewa yanzu ya koma Khairat Night Club da aiki"
"Yaushe ne?"
"Bara ne (shekara daya)"
"Amma ka ta'ba zuwa Khairat d'in gunsa?"
"Eh naje,amma da na tambayi masu gadin sai suka cemin babu wani Abubakar dake aiki agun"
"Lokacinda ka ganshi a filin polon ya kaga yanayinsa,irin na masu kud'ii ne?"
"Eh to gaskiya dai ya canja bai yi kama da mai aikin wahala ba"
"Nagode"nace dashi sannan na dawo mota. Hankalina ne ya rabu biyu a yayinda nake tunanin wajen zuwa "Khairat ya kamata naje ko kuma can Tsamiyar bokan wajen da aka ce ya zauna?" Daga 'karshe na yanke shawarar zuwa Tsamiyar bokan. Na tambayi mutane da dama amma babu wanda ya sanshi a layin dole na ha'kura na dawo gida lokacin dare yayi.
Washe gari da misalin goma da rabi na isa Ma'aikatar ilmi (Ministry of Education) tarun tulin 'yan sandan da na ganine da makamai a hannunsa ya tayar min da hankali mutane a gefe suna kallo a yayinda ake caje wasu. Matsawa nayi kusa da wani nake tambayarsa "Malan me ke faruwa anan ne?"
"Ina tunanin 'yan fashi ne suka kawo hari"
"Yan fashi !Me suka zo sata?"
"Ban sani ba"
Ana haka ne na hangi mutuminda yace na dawo yau bayanmun gaisa nake tambayarsa "wai 'yan fashi ne suka zo muku?"
"A'a ba 'yan fashi bane"
"Su wanene to?"
"Wanine yazo yake son sace mana files sai dai ya kashe d'aya daga cikin masu gadinmu a yayinda ya raunata 'dayan da harsashi a kafad'a"
"Amma taya akai kuka san file yazo sata?"
"Saboda a wajenda muke ajiye files 'din abun ya faru sannan an warwatsa file din zuwan 'yan sanda ne ya koreshi daga wurin"
"Yanzu kenan baku sani ba ko ya sace file d'in?"
"Shine binciken da mukeyi kenan"
"To ya maganarmu ta jiya?"
"Wallahi ban duba saboda faruwar wannan al'amari,amma me yasa kai kuwa kake son a binciko ma file dinta?"
"Wato wani 'dan uwana ne ya jima da barin gida bai dawo ba shine aka turoni nemansa na tattambayi mutane da dama sun fad'amini cewa suna tare da ita Hadiza Abdullahi Adamrin shi yasa nake son a bincikomin file d'inta ko zan ga adreshin gidan da suke zaune"na shimfid'da masa karya. Gyad'a kansa kawai yayi alamar ya gamsu kafin daga bisani yace "amma me yasa bazaku sanar ma 'yan sanda ba?"
"Eh muna 'ko'karin hakan,amma yanzun dai muna bukatar file d'in"
"To yadda za'ayi ka dawo anjima misalin 'karfe biyu (02:00pm) insha Allah zan bincika ma"
"Nagode"
Gida na nufa domin na huta kafin lokacin ya cika saboda matsananciyar gajiyar da ke damuna. Gumi ne ya fara ketowa daga kaina zuwa goshina a lokacin da na hango wasu 'yan sanda su biyu a unguwartamu kusa da gida. Naso na koma da baya saboda ina ji a jikina ni d'in mai laifi ne ko dan akan kisan Laila da saurayinta da akai amma na fasa. Haka nazo ta kusa dasu na nufi gidana a raina ina jira naji sunce you are under arrest amma shiru babu wanda yace ci kanka a cikinsu har na shiga gida. Hankalina bai kwanta ba kwata-kwata jira kawai naji an 'kwan'kwasa min 'kofa amma shiru can na leka da taga sai na hango suna wucewa zasu bar unguwar. Sai da na tabbatar sunyi nisa sannan na fito na samu wani ma'kocina nake tamnbayarsa abinda ya kawo su "wai neman wata yarinya suka zo,tace musu anan unguwar take"yace dani. Tsaki nayi gami da sau'ke wani nannauyen ajiyar zuciya sannan na dawo gida.
'Karfe biyu daidai na isa wurin,wannan karon akwai 'karancin mutane a wajen sannan 'yan sandan ma basa nan. Kai tsaye na shige ofishinnasa bai jira na zauna ba ya mi'kamin wata doguwar takarda fara cike da rubutu a 'bangare 'daya. "Hoton fa?"Nace dashi
"Babu hoto a file 'dinta"
"To nagode"
A mota nake nazarin takardar anan naga abinda yaja hankalina Busuku,kirikasa
mma Local Govt jigawa state shine garinsu ai kuwa Jamila ma can ne tace garinsu. Bayan na ci gaba da duba takardar ne naga makarantar da ta halarta private commercial college a birgade. Ban jira ba kawai na nufi makarantar ganin lokacin tashi yayi ko Allah zai sa na iske malaman. Office d'in principal na shige
Malam barka da aiki"nace dashi bayan nayi sallama
"Yauwa,ya akayi?"
"Ni d'an jarida ne daga mikiya,nazo inaso a bincikamikn file d'in wata d'alibarku saboda muna so zamu d'auki wasu bayanai ne game da ita"
"Ok! Amma taya zan san kai d'an jarida ne"
"Ga I D card d'ina"na mi'ka mar
Bayan 'yan wasu sakanni ya mi'ko min sannan yace "ya sunan yarinyar,kumna tun yaushe ta bar nan?"
"Sunanta Hadiza Abdullahi Adamri shekaru goma kenan rabonta da nan"nace dashi a lokacin da na duba takardar dana kar'bo a ministry. 'Kararrawa ya kad'a masinjan sa ya shigo
"'Dahiru kaje ka sami malam bala ku wuce store wajenda muke ajiye file na yara ku dubomin me wannan sunan ka kawo yanzu. Amma shekararta da goma da barinnan"yace masinjan bayan ya shigo
Surutai ya rufeni dasu na makarantar tun daga farkonta har zuwa yanzu,kamar yadda yake fad'amin ainahi mahaifinsa ne ya gina makarantar kafin ya gajeshi. Shigowar masinjan ce ta ceceni daga surutannasa da ba fahimtarsu nake
"Yallabai gashi"
"Yauwa"yace da maigadin a lokacin da yake kokarin karbar file din
"Zainab Abdullahi Adamri ! Wannan ai ba shi bane Hadiza Abdullahi Adamri na ce ma ba Zainab ba maida ka ku d'auko na Hadizan"yace da masinjan yana 'ko'karin mi'ka masa file d'in.
"Malam zanso na duba wannan d'inma kafin su binciko waccan"nace dashi
"Ba nata bane ba fa"
"Eh na sani amma ina jin kamar suna da ala'ka"
"Ok ! Gashi to"
A lokacinda nake bincika file d'inne masinjan ya shigo a karo na uku ri'ke da wani file 'din "yallabai gashi"ya mi'kawa principal 'din. Bayan na 'karba ne na fara dubasu. Babu wani banbanci tsakanin file 'din biyu na daga adreshinsu komai 'daya ne hatta sunan mahaifiya (fatima). "Ko zan iya kwafar wasu abubuwa a jiki?"Nace da principal d'in
"Ba matsala"
A 'kasa ne na zo wajen halayya da d'abi'unsu ita Hadiza nutsatstsiyace sannan tana da haza'ka sai dai tana da saurin fushi ita kuma Zainab bagidajiyace sannan jaka ce.
"Malam ko kuna da hotonsu?"
"A'a bama ajiye hoto"
"To nagode malam zan koma"nace dashi na mi'ke tsaye bayan na gama kwafa.
Zama nayi a cikin mota ina nazari. Duk yadda akayi matar Jaheed Auwal 'yan biyu ne,amma wacece Jamila tunda ita tace ita kad'ai ce agun iyayenta????