TSEGUMI-09
.
Washe gari da misalin 'karfe tara na isa Tahir guest palace kamar yadda Laila ta fa'damin nan ne wajenda tayi kafin ta taka wani 'kulli. Anan na had'u da wata ma'aikaciyarsu nake tamabayarta bayan na dam'ka mata dari biyu a hannunta a matsayin cin hanci. "Wata nake tambaya Hadiza ance ta ta'ba aiki anan"
"Hadiza?"
"Eh"
"Eh ta ta'ba aiki anan amma ta bari"
"Ko zan iya sanin wajenda ta koma?"
"Gaskiya ban sani ba,amma dai ga wani shago can tsallaken titin ka tambayi mai shagon zai iya sani domin mutumiyarsa ce"tace dani.
"Malan barka dai"
"Yauwa"
"Ina tambayar Hadiza ne da ta ta'ba aiki anan tahir guest palace"
"Ai ta jima da barinnan"
"Eh na sani,ina son naji ko ka san wajenda ta koma da aiki"
"Amma lafiya kake nemanta?"
"Lafiya lau,ni 'kanin mahifiyarta ne daga 'kauye. Ta jima bata je gida bane shine akace na fito na nemeta"na shirga mar 'karya
"Gaskiya ta bar nan shekaru uku da suka wuce,akwai lokacinda naga an buga mutuwar wata mata a jarida na 'dauka ma ita ce sai naga sunan ya bambanta kuma ita Hadiza daga Jigawa take sa'banin ita waccan dake Kaduna"
"Ka santa ma kenan?"
"Sosai ma,ai mutuniyatace"
"Ta ta'ba fad'ama wani waje da ta ta'ba yin aiki kafin tazo nan?"
"Eh"
"Ina ne"
"Ta ta'ba aiki a Ministry for Education"
"Amma lokacinda zata bar nan,ko ta fad'ama wajen da zata koma?"
"Bata fa'damin ba saboda yanayin yadda ta bar nan 'din"
"Wanne yanayi kenan?"
"Ka duba kaga duk yadda muke da ita lokaci guda kawai naga tana kayakin a boot 'din wata farar mota babu ko sallama ta wuce"
"Wacce kalar motace?"
"B. M. W ce fara,motar ta burgeni matu'ka har sai da na rubuta lambarta a jikin bango ma"
"Yanzu haka kana da lambar?"
"Eh akwai bari na duba ma". Nan ya fara dube-dube na 'yan wasu lokuta
"Yauwa gata nan"bayan na rubuta lambar na masa godiya. A hanya na kira jabeer
"Kayi ha'kuri fa Jabeer zaka na dameka,wallahi wata lamba nake so ka 'kara bincikomin"
"Babu komai,fadamin lambar kawai"bayan kamar minti goma ya kirani
"Ina jinka"nace dashi
"Motar mallakin Jaheed Auwal ce" shiru nayi ina tunani bance 'kala ba
"Hello kana jina?"Yace dani
"Eh ina ji,kace ta Jaheed Auwal ce?"
"Eh"
Yanzu kuma na gane cewa Hadiza Abdullahi Adamri itace Fatima Jaheed shine aka canja mata suna daga hadiza zuwa Fatima duk dan a rufe sirrinta. To amma wacece Jamila ko duk ita ce Hadizan,babu ta yadda za'ayi ace Jamila itace Hadiza domin naga gawarta. To ko dai ita Hadizan a gidan marayu ta taso data girma shine ta gudu? Ko kuma guduwa tayi daga gun iyayenta? Tunanina ya tsaya a lokacinda na tuno da cewa ai ita ma Jamilar 'yar Jigawa ce (Busuku) amma ai ita tace a gaban iyayenta ta taso wa'danda suka mutu tana da shekara goma sha biyar daga nan ta dawo hannun ma'kociyarsu wacce ta gudu ta barta daga baya. Babu ta yadda za'ayi ace Jamila itace Hadiza na tabbatarwa da kaina haka.
Yanzu dai kam na gano cewa Hadiza Abdullahi Adamri ita ce Fatima Jaheed. Amma wacece ita? Su wanene iyayenta?Har yanzu suna da rai? Da ace zan ga hotonta to da duk abin zaizomin da sauki. Sai a sannan kuma na tuna Auwal da aka kashe ta dalilin hoton da kuma mutumin da ke bibiyata. Babu shakka sai na taka a sannu
Kai tsaye gidan Laila na nufa don cika mata 'dari ukun ta 'karasa fad'amin wajen da zanga Hadiza. Sai da na 'kwan'kwasa 'kofar a 'kalla sama da sau goma amma ba'a bude ba. Ga mamakina ina tura 'kofar naga ta bud'e kutsa kaina ciki kawai nayi. Tsulum naji na tsoma 'kafata a wani abu kwance a kan katifa Laila ce da Babannan idanunsu yana kallona. Sai a sannan na lura da 'dan 'karamin tafkin jinin da ke malalowa daga kan katifar zuwa inda na ajiye kafafuna. Suma an kashe su!!!!
Da gaggawa na fice a 'dakin na bar layin unguwar. A hanya nake ta nazarin mutumin dake wannan aika-aikar. Babu shakka 'yan sanda zasu iya nemana a matsayin primary suspect musamman idan akayi rashin sa'a suka had'u da matar da ta kaini har bakin 'kofar 'dakin Lailan jiya. Tunanin karbar hayar motane yazomin saboda irin yadda nake fama da jigila daga nan zuwa can amma bani da isassun kud'in da zan karbi hayar motar dashi dole na na biya wajen A'isha ta ara min dubu goma. Bayan na karbo hayar motar ne na wuce kai tsaye ma'aikatar ilmi (Ministry of Education). Ta cikin mirrow ina tafiya na hangi blue peugeot 'dinnan tana biye dani nesa kad'an daga wajen da nake. Isata ma'aikatar nayi fakin 'din motar a gefe sannan na fara dube-duben motar da ke biye dani amma ban ganta. Wajen maigadin wurin na nufa bayan mun gaisa nake tambayarsa gameda Hadiza Abdullahi Adamri amma yace bai santa ba sai dai ya kwatantamin office d'in wani clerk. A ciki ne na iske wani saurayi zaune a kan kujera yana ta faman dube-dube cikin wasu file,bayan mun gaisa ne yamin iso a 'daya daga cikin kujerun na zauna nima
"Yauwa lafiya?"Yace dani
"Wani taimako nake so zakamin idan da hali"
"Allah yasa zan iya"
"Ameen,akwai wata Hadiza Abdullahi Adamri wadda ta ta'ba aiki anan shekaru shida zuwa bakwai da suka wuce shine nake so ka taimaka ka binciko min file 'dinta"
"Gaskiya bama bada file 'din ma'aikatanmu"
"A'a ba wai ina nufin a ban ba,kawai inaso ne ka bincikomin makarantun da ta halarta adreshinta da kuma wakilanta (next of kin) idan da dama ma hotonta wadda nasan baza'a rasaa ba"
"Gaskiya bazai samu ba yanzu saboda yanzu haka akwai ayyuka a gabana,amma ka dawo gobe bayan 'karfe goma Insha Allah kafin lokacin zan binciko ma"
"Nagode"nace dashi sannan na fito daga office 'din