Gaskiya Dokin Karfe

Galadima.com.ng Domin sharhi kan al amuran yau da kullum

TSEGUMI 08

TSEGUMI-08
.
Kai tsaye titin freedom 'din na nufa,sai dai kafin na isa a hanyata sai da na kira abokin aikina Ibrahim na sanar dashi game da motar da ke ta bina. Lambar wani abokinsa ya aikomin wanda ke aiki a Licence office,ban 'bata wani lokaci ba na kirashi aka sadani dashi.
"Hello"aka amsa
"Hello jabeer ne"nace dashi
"Eh shine"
"Ibrahim abokinka dake aiki a jaridar Mikiya ne ya ban lambarka,sabodaina so zaka taimakamin"
"To ina jinka"
"Ina so nasan mamallakin wannan motar"na karanto masa lambar.
Bayan kamar da'ki'ka goma ya kirani "motar haya ce"
"Kasan address 'dinsu?"
"Eh,Dauda car hire agency ofishinsu yana zoo road (DCHA)"
"Yauwa,nagode sosai"nace dashi sannan na katse wayar naci gaba da neman gidan Laila. Nasha wahala kafin na isa gidan,babban gidane hawa biyu da alama gidan haya ne a daidai mashigar na iske wani kul'be'ben mutum "malam don Allah ina tambayar Laila ne"
"Ka hau sama"yace dani. A can saman benen ne nake tambayar wata mata Laila,sai da ta kaini har 'kofar 'dakin tace min shine 'dakin Laila. Na 'dan 'dauki lokacin ina 'kwan'kwasawa kafin daga bisani wani matashi ya bud'e 'kofar a fusace. Daga shi sai gajeren wando da singileti ya dubeni sama da kasa sannan yace "ya akayi ne"
"Ina tambayar Laila ne"
"Waye kai?"
"Ni abokin Hadiza ne 'kawar Lailan" ya bud'e baki da niyyar sake min wata tambayar aka katse shi daga ciki "Babannan barshi ya shigo". Yanayinda na sameta a cikinne na tabbatarwa da kaina bata da wani bambanci da karuwa,a kan wata kujera na zauna irin ta katakonnan da alama ita kad'ai ce a dakin domin suma sai a kan katifa suka zauna idanunta 'kyar a kaina sai kace mujiya
"Hadiza ce ta aiko ka?"Tace dani
"A'a ina dai nemanta ne shine aka kwatantamin ke aka ce kinsan wajenda zan sameta"
"Amma kai waye?"
"Ni 'dan jarida ne,ina so zamu 'dan tattauna da ita ne akan wani abu sannan mu biyata"
"Malam dan Jarida kace kana neman Hadiza domin 'daukan wasu bayanai sannan ka biyata,to nawa ni kuma zaka biyani idan na kwatantama wajen da zaka sameta?"Tace dani cike gautsi
"Nawa kike so"
"Dubu 'daya"
"Kai ! Gaskiya bani da dubu yanzu,ina laifinma 'dari hud'u"
"mtswwww"taja wani dogon tsaki sannan ta dubi abokin holewarta tace dashi "babbannan bud'e masa 'kofa ya fita"
Dama bai so zuwana ba da 'karfi-'karfi ya kama hannun rigata yana 'ko'karin figata waje "dakata"nace dashi
"Zan bada 'dari bakwai
"Idan kuwa hakane to zan fa'dama wasu abubuwa gameda ita amma ba duka ba,saboda kasan Hadiza shegiyace tana da masifar wayo. Inaso nai maganintane kafin ta....ta katse abinda take son fad'a
"Kafin ta me?"Na tambaya cike da 'kaguwa
"Ina 'dari bakwai 'din"
Da gaggawa na cirosu daga walet na mika mata.
"Kaje Tahir guest palace sokoto road,nan ta koma da aiki lokacinda ta bar Al'amir restaurant. Amma bata jima da barinnan bama saboda wani 'kulli da ta taka. Babu wanda yasan wajenda ta koma ko kaje nan sai ni,ni kuma bazan fad'a ba sai ciko 'dari ukun"
Dubu da 'dari biyu ne kacal suka rage min a jikina,kuma dasu ne nake son nayi 'kud'in mota zuwa wajen Garba Hadi siyan hotunan Hadiza. "Yanzu haka babu kud-n a jikina,amma da wanne lokaci zan dawo na sameki?"
"Ka dawo gobe misalin sha 'daya na safe"
Wani mutum na gani yana sauka daga benin a daidai lokacinda nake fitowa daga 'dakin yayi shigar ba'ka'ken kaya over size kansa rufe da ba'kar hular sanyi ya zura hannayensa a aljihu da sauri ya sauka daga benen "kodai shine ke bina a mota"nace a raina a lokacinda na rufa masa baya. Ko alamarsa ban gani ba a farfajiya da wajen gidan. Wani na samu a waje nake tambayarsa ko yaga fitowar wani mai ba'ka'ken kaya
"Naga shigarsa dai,'kila ko ta 'kofar baya ya wuce"
"Akwai 'kofa daga baya?"
"Eh akwai"
Ganin 'kuratowar da lokaci yayi ne yasa na kama hanyar gidan Auwal kamar yadda yace nazo bakwai dot. Na isa unguwar da misalin shida da rabi,wajen wata mai saida a wara na zauna ina jiran cikar lokacin kafin na 'karasa. A raina ina ta sa'ke'ken Hadiza Abdullahi Adamri ko ita ya kamanninta suke yau dai zan gani. Bakwai saura minti biyar nabiyo kwararon har bakin 'kofar 'dakin kamar yadda ya kwatantamin. 'Kwan'kwasawa nayi hade da sallama amma shiru,agogon hannuna na duba naga bakwai daidai ban haura ba "kar ace bayanan,ai kuwa da bai kyautamin ba"nace a raina. Na 'dan 'dauki lokaci mai tsawo ina bugawa amma shiru,kofar 'dakin na kama da niyyar gwada bud'ewa amma ga mamakina sai naga ta bud'e. A zaune a kan kujera Auwal ne fuskarsa da alamun murmushi a fuskarsa "Auwal baka ji inata buga 'kofa bane amma ka......"Bakinane ya 'kafe harshena ya sar'ke a lokacinda idanuna sukayi arba da jinin da ke 'bul'bulowa daga 'kirjinsa saitin zuciya. Babu shakka ya mutu
Lura da yanayin gawar ne zai tabbatar maka da cewa ba'a jima da kashesi,amma waye ya kashe shi?
Sai a sannan na lura da irin yadda aka birkita komai na gidan,gaba-ki-'daya an warwatsa kayansa na sawa ko ina takardune zube a kowanne 'bangare na 'dakin. Lura da yanayin gawar ne zai tabbatar maka da cewa mai kisan ya 'kware wajen iya harbi,saboda harbi 'daya ya mar wanda yayi sa'ar samun sa a 'kahon zuciya. Duk yadda akayi wanda yayi kisannan ya biyo sawun hotunan Hadiza ne kuma da alama ya 'daukesu ya gudu. Gudun taka sawun 'barawo ya sani zaro hankici daga aljihuna na goggoge bakin 'kofar da na 'taba yayin shigowa da fita a tsorace na bar layin unguwar cike da tunani a raina. Cikin ikon Allah babu wanda yaga fitata
Zoo road na nufa domin binciko wani abu gameda motar da ke bina ina ji a jikina bazata rasa nasaba da kisannan ba, a hanya nake tamabayar kaina "an birkita gidana an dau'ke hoton Jamila gashi kuma nan ma an 'dauke na Hadiza shin suna da had'i ne? Amma kuma wanene zai sace hoton Hadiza? Wanne irin muhimmancine da hoton da har zai sa a kashe mutum saboda shi? To ko dai Hadiza abdullahi Adamri ita ce Fatima Jaheed? Idan kuwa har Hadiza itace Fatima Jaheed babu makawa Alh Jaheed Auwal ne ke turowa a kwashe hotunanta don kare mutuncin kansa na auren 'yar gala ko ince karuwa da yayi musamman kasancewarsa babban mutum na tabbata babu wani mutum da zai so ace matarsa da yake matu'kar so ta ta'ba yin karuwanci ko makamanci haka. 'Kila shi yasa ma babu wani cikakken bayani na tarihin rayuwarta a jaridar da ta buga kisanta. Haka a invitation card na aurensu ma kawai sawa akayi Jaheed weds Fatima babu wani sunan iyayenta da aka sa. "To amma idan Jaheed 'dinne taya akai yasan zamu ha'du da Auwal 'din misalin 'karfe bakwai? Da irin wa'dannan tunane-tunanen na isa Zoo road.
Ban sha wahala ba wajen gano wajen hayar motocin a ciki ne na had'u da wani saurayi da alama shima ma'aikacinsu ne "malan barka dai"nace dashi
"Yauwa"
"Don Allah tambaya nake"
"Ina jinka"
"Anan ne aka 'karbi hayar motar nan ko"nace dashi a lokacinda nake nuna masa lambar motar
"Eh nan ne,lafiya ko wani abu ne ya faru"
"A'a babu abinda ya faru,kawai ina so nasan wanda ya 'karbi hayarta ne"
"Ina zuwa"yace dani a yayinda ya koma ciki
"Basheer Shehu"yace dani bayan ya fito
"Ok ! Amma adireshinsa fa"
"A na'ibawa yake gida mai lamba 23 kusa da police station"
"Tun yaushe ne ya 'karbi hayar motar?"
"Jiya kamar yanzu" na duba agogo naga 'karfe takwas na dare
"Yaushe kuke rufewa?"
"Goma na dare"
"Amma ya dawo muku da motar ne?"
"Eh ya dawo da ita"
"Da wanne lokaci?"
"'Dazunnan da misalin 'karfe shida da rabi na"
"Ko zaka iya kwatanta kamanninsa?"
"Eh gajere ne baki mai jiki"
"Wad'anne kalan kaya ne a jikinsa?"
"Doguwar rigace fara da blue jeans"
Ko ka'dan baiyi kama da mutumin da na gani ba a gidan Laila domin waccan 'din dogo ne sanye da ba'ka'ken kaya sannan da gashin baki a fuskarsa.