TSEGUMI-07
.
Sai da na fara kunna wuta sannane tsorona ya dad'u saboda ganin irin yadda aka birkita komai na gidan. "Da alama 'barayi ne" nace a raina,nan na fara binciken abubuwan da aka 'dauka amma ga mamakina basu 'dauki wani abu mai muhimmanci ba idan banda rediyo ta tajin labarai sai dubu na 'daya dana ajiye cikin dirowa. Tunanin hotonne ya fadomin aguje na wuce 'dakina dubawa,'dakin ma an birkita. A 'kasa na tarar da littafin da na ajiye hoton amma ga mamakina sai banga hoton a ciki ba. Sai da na bincika ko ina na 'dakin amma banga alamar hoton ba. "To ko hotonma 'barayin sun 'dauka?Wanne amfani to zai musu idan suka dauka?
Nayi matu'kar ta'kaicin 'batan hoton,dashi ka'dai zan iya bambance tsakanin Hadiza da Jamila. Da ace na kai masa hoton ya tabbatar min da cewa Hadiza ita ce Jamila to da abubuwan zasu zomin da sauki. Sai dai har yanzu ina ji a jikina cewa Jamilar itace Hadiza,amma me yasa ta canja sunanta,tayaya mijinnata ya tara kud'in da zai gina irin wannan katafaren gidan sha'katawar da sauran kadarori a cikin shekaru shida kacal,alhali duk sana'o'insa ba wasu manya bane da zasu kawo masa kud'I. To ko dai safarar miyagun 'kwayoyi yake,da irin wad'annan tunane-tunanen na sake dawowa falo. Tunanin sanar da 'yan sanda abinda ya faru dani ne ya fad'omin,amma nayi fatali da ita kasancewar abubuwanda aka sacen ba wasu abubuwa ne masu tsada ba.
Bayan na zauna a 'daya daga cikin kujerun dakae falon tunanina ya fad'ad'a akan Fatima Jaheed. Ya kamata itama na binciko wani abu game da ita musamman danginta. Sai dai matsalar babu wani cikakken bayani gameda ita ko iyayenta a jaridar mu da ta watsa labarin sacewarta da kasheta da akayi.
Nayi 'ko'karin kai ziyara wasu daga cikin ma'aikatun jaridun dake garin (kano)amma babu 'daya daga cikinsu da na samu wani cikakken bayani gameda Fatima Jaheed ko na iyayenta. Hakanne ta sani yanke shawarar zuwa wajen Garba Hadi (wanda zan kawowa hoto). Bayan mun gaisa nake sanar dashi cewa na samu matsala gameda hotonnan amma zanci gaba da bincikawa idan na samu zan kawo ya dubamin ko ita ce. Sai dai kafinnan ina so zan tambayeshi inda Abubakar yake da zama shi da budurwar tasa Hadiza Abdullahi Adamri. Kai tsaye unguwar da ya kwatanta min na nufa,anan na iske wata mata a daidai layin da ya fad'amin.
"Malama barkanki dai"
"Yauwa"
"Don Allah tambaya nake"
"Allah yasa na sani"
"Ina tambayar wani Abubakar Garba da suka ta'ba zama anan shida wata Hadiza Abdullahi Adamri"
"Eh na sansu,amma sun jima da barin nan"
"Amma kin san ita Hadizan?"
"Eh na santa man,tare suke ai"
"Ko zaki iya kwatanta kamanninta"
"Gaskiya ban iya kwatanta kamannin mutane ba amma dai kyakkyawa ce"
"Fara ce ko ba'ka?"
"Tsaka-tsaki ce gaskiya"tace dani. Ai kuwa jamila ma tsaka-tsakin ce nace a raina
"Tana aiki?"
"Eh tana aiki a wani restaurant"
"To amma da zasu bar unguwarnan ko sun fad'a muku inda zasu koma?"
"A'a babu wanda suka fad'ama hasalima da bashin maigidan hayan suka gudu basu biya ba"
"Amma babu wasu muatane dake kawo musu ziyara?"
"Akwai su sosaima,sai dai bamu damu da sanin ko su wanene ba,saboda ko kad'an bamu saki jiki dasu ba"
Kwatancen restaurant 'dinda tamin na nufa,sai dai a hanya kafin na 'karasa titi nake ji a jikina kamar wani na biye dani. Bayan na waiga ban ga kowa ba naci gaba da tafiya har zuwa titin,anan na hau mota zuwa restaurant din. A cikin motar ne na lura da wata mota peugeot blue,sai dai bazan iya shaida matukin motar ba sakamakon tintin 'dinda ya lullu'be gilasan motar. Lambar motar na sake dubawa DCHA aka rubuta a jikin lambar.
Bayan na sau'ka a daidai wajen,kaina tsaye na isa restauranta 'din. Anan na had'u da wata mata nake tambayarta
"Don Allah ina tambayar wata Hadiza Abdullahi Adamri wacce ta ta'ba aiki anan shekaru shida da suka wuce"
"Wallahi ban jima anan ba nima,sai dai kaje wajen waccan ka tambayeshi zai iya saninta domin ya jima anan. Sunansa Auwal"
"Malam barka dai"
"Yauwa"
"Ina tambayar Hadiza Abdullahi Adamri ne"
"Tab! Hadiza ai ta jima da barin nan"
"Ko kasan wajenda ta koma da ta bar nan?"
"Eh na sani,Al-amir restauranta dake sharad'a phase1 ta koma da aiki"
"Amma me yasa kake nemanta?"Yace dani
"Babu komai kawai muna son biyanta ne akan wani talla na kamfaninmu da tayi"na kifar dashi
"Kamfanin sabulu kake aiki?"Yace dani
"A'a,amma me yasa ka tambaya?"
"Naga sune masu sa hotunan kyawawan 'yan mata,ganin itama kyakkyawar ce yasa na tambaya"
"Hmmm hakane,amma kana da hoton ta ne?"Nace dashi
"Ina dasu dayawa ma idan zaka siya,sai dai suna gida"
"Don Allah kwatantamin gidannaka zan dawo anjima"
"To amma kar ka haura 'karfe bakwai na dare"yace dani bayan ya rubutamin adreshinnasa a takarda.
Akan hanyata ta zuwa sharadan a cikin bus idanuna suka sake arba da blue peugeot d'innan. "Ko dai ni suke bi?"na tambayi kaina. Har na isa daidai wajen motar na biye dani sai dai nesa-nesa take da motar da nake ciki. Ban sha wahala ba wajen samun Al'amir restaurant din,ciki na shiga kai tsaye. Bayan mun gaisa da wata mata mai dan matsakaicin 'kiba ne nake tambayarta
"Malama ina tambayar wata Hadiza Abdullahi Adamria,ance ta ta'ba aiki anan"
"Eh amma gaskiya tunda ta bar nan ban sake ganinta ba"
"Ko kin san inda ta koma?"
"A'a amma dai akwai wata 'kawarta Laila wacce ke zuwa tana fita da ita"
"Ita Lailan kin santa ne?"
"Eh gidanta yana daidai layin freedom,amma dai 'yar gala ce"
"Menene kuma gala?"
"Irin masu rawar nan a gidajen cinema"
"Ok !Amma kina ganin itama Hadizan galar ta koma?"
"Eh zata iya kasancewa"
"Nagode"nace da ita a lokacinda na fito daga restauranta 'din. Ina 'ko'karin tafiya titin freedom radio ne na sake hango blue peugeot 'dinnan nesa dani