Gaskiya Dokin Karfe

Galadima.com.ng Domin sharhi kan al amuran yau da kullum

TSEGUMI 06

TSEGUMI-06
.
Isata daidai mashigar kamfanin na had'u da wani mutum cikin Uniform an rubuta security (maigadi). Bayan na masa sallama muka gaisa,nake tambayarsa "Mal. Don Allah tambaya nake"
"To Allah yasa na sani"
"Ina tambayar wanine Abubakar Garba,ya ta'ba aiki anan shekaru shida da suka wuce"
"Shekaru shida kace?"
"Eh"
"Kuma kazo nemansa nan"
"Eh nasan yanzu haka baya tare daku,ina nufin ko zan had'u da wani wanda ya sanshi"
"Gaskiya banajin akwai"
"Amma ai kuna da record book da kuke rubuta sunaye da adreshin masu kaiwa ma'aikatanku ziyara kafin su shiga"
"Eh muna dashi"
"To don Allah ko za'a bincikamin irin mutanen da ke zuwa masa ko Allah zaisa na samesu su sadani dashi"
"Gaskiya bazai yiwu ba saboda aiki nake"
"Kar ka damu nace dashi a lokacin da na zaro naira dari biyar na dam'ka masa a hannu"
"To shikenan ba matsala,amma ka dawo bayan Azahar zan bincika ma"
Da misalin 'karfe biyu na koma,ina zuwa ya taryeni hannunsa ri'ke da takarda. 'Damka min takardar yayi sannan ya juya a saye da alama baya so wani ya gani.Ina 'ko'karin bud'a takardar ya juyo yace dani "kaje can wani wurin sai ka duba". Da na tabbatar nayi nisa da wurin na fiddo da takardar na fara dubawa,sunayen mutanene birjik a jiki da adreshinsu.
Tun daga wannan lokacin na fara bin adreshin mutanen dake jikin takardar amma babu 'daya daga cikinsu da nayi sa'ar samu daga ace ya bar unguwar ko kuma kaji ance bamu sanshi ba. Misalin 'karfe biyar da rabi na isa rijiyar lemo daidai 'yan katako,don bibiyar wani mai suna Garba Hadi wanda shima sunansa na jikin takardar. A cikin lungu gidannasa yake,da alama gidan haya ne irin na yaku bayinnan. A daidai 'kofar na tsaya na 'kwan'kwasa,wani shirgegen 'kato ne ya fito daga gidan na tsorata ainun da siffarsa "wanene ke 'kwan'kwasa mana 'kofa"yace dani a fusace yana ta faman huci
"Nine"nace dashi cike da karaya
"Ya akayi to"
"Ina tambayar Garba Hadi ne"
"Lafiya kake nemansa?"
"Eh lafiya,ina so ne zai sadani da abokina wanda na samu labarin abokinsa ne shima kuma yana zuwa gunsa lokacinda yake aiki a kamfanin takalma na Jogana"
"Wanene abokinnaka"
"Abubakar garba"
"Garba Hadi baya gari amma gobe ko jibi zai dawo,sai dai ko ka leko goben idan ya dawo"
"To nagode"nace dashi sannan na dawo gida.
Na jima a zaune ina nazarin mafita,domin dai duk wahalhalun da nasha babu wanda na samu wani abu 'kwa'k'kwara da zai tabbatar da wani abu gameda ita. Hannuna na zura a aljihu na 'dauko takardar ina nazarin sunayen mutanen da ban samu zuwa wajensu ba. A can 'kasa 'karshen shafin farko idona suka hango min da sunanda yayi sanadiyyar katsewar bugun da zuciyata take na 'yan wasu dakikai. "Hadiza Abdullahi Adamri" na maimaita sunan a bakina,wacece kuma haka kodai sunan Abdulllahi Adamrinne yazo daidai dana Jamila Abdullahi Adamri? Ko kuma dai itama danginsu 'daya da Jamilar? Na tambayi kaina. "Amma kuma ai ita jamilar ta fadamin cewa bata da kowa,ita kadaice gun iyayenta. Hasalima tana da shekara goma sha biyar iyayenta suka rasu lokacin tana aji biyar na secondry. Wata makociyarsu ce ta riketa har ta gama kafin ta gudu ta barta saboda tsangwamarta da take kamar yadda ta fadamin a tattaunawarmu,amma itama tace min sun had'u da tsohon mijinnata shekaru shida da suka wuce itama kuma wannan ta had'u dashi shekaru shida da suka wuce. Wai yaya abin yake?"Na tambayi kaina.
.
Washe gari da misalin shida na yamma na koma neman Garba Hadi. "Wanene"aka ce dani daga ciki
"Nine wanda yazo neman Garba Hadi jiya"
Su biyu suka fito wannan karon shi da wani gajere "kai ne kake neman abubakar Garba"gajeren yace dani yana nazarin yanayina
"Eh nine"
"Amma kai abokinsa ne?
"Eh abokinsa ne ni,ban jima da dawowa daga America ba"na shirga masa 'karya
"Amma taya akai kasan na sanshi?"
"Acan kamfanin da yayi aiki aka kwatanta min wajenka,sunce kana zuwa gunsa"
"Hakane,amma gaskiya yanzu rabona dashi shekaru hudu kenan ban sake ganinsa ba. Tun wani sa'bani da muka samu dashi akan wata budurwarsa,sabo
da irin yadda take jefa rayuwarsa cikin garari domin biyan bukatarta yasa na bashi shawarar ya rabu da ita amma ya'ki. Tun daga nan muka raba gari"
"Ya sunan budurwar tasa kuwa"
"Sunanta Hadiza"
"Zaka iya ganeta idan kaga hotonta?"
"Sosai ma"
"To don Allah gobe zan dawo da hoton saboda yanzu bana tare dashi"
"Babu matsala"
Da alama zan warware rud'un da ke tsakanin Hadiza da Jamila. Tunanin zuwa gidan cinema ne ya fad'omin domin 'debe kewa ko na samu na sassauchi a kaina wanda tuni har na fara sabawa da ciwon da yakemin. Ban dawo gida sai misalin sha 'daya da rabi na dare a nan naga abinda ya matukar tayarmin da hankali. 'Kofar gidannawa na gani a bud'e alhalin ina da tabbacin sai da na kulleta kafin na fita. "Waye a ciki" na fad'a da karfi amma shiru babu wanda ya amsa. Sosai na tsorata,tuni gumi ya fara ji'kamin riga "kodai Jaheed ne ya aiko da yaransa su kashe ni,amma kuma ai kwanakin basu cika ba. A hanakali na 'karasa bakin 'kofar cikin sand'a na shiga cikin gidan.