Gaskiya Dokin Karfe

Galadima.com.ng Domin sharhi kan al amuran yau da kullum

TSEGUMI 05

TSEGUMI-05
.
BUSUKU shine 'kauyen da ya kamata na fara kai ziyara domin nanne garinda Jamila Abubakar tace dani shine garinsu a tattaunawar da mukayi da ita a can jahar Jigawa,kirikasamma local Government. A gaggauce bayan na had'a kayana a jaka ina shirin tafiya naga dacewar sanar da Maryam gameda tafiyartawa saboda kada taga shiru kwana biyu,wayata na 'dauko na mammatsa lambobinta kasancewar tuni na haddacesu a kaina sannan na karata a kunnena ina jiran ta sadani da ita
"Hello"ta amsa
"Maryam"
"Sweetheart yau ba baby 'din da ka saba kirana dashi ma,kodai nai maka laifine?"
"Sorry,wallahi kan nawane sai a slow,yanzu hakama na bugone na sanar dake tafiya ta kamani zuwa Jigawa domin 'daukar wasu rohoto. Saboda kar kiga shiru kwana biyu.
"Amma yaushe zaka dawo"
"Inajin bazan wuce kwana biyu ba gaskiya"
"To!Allah ya kiyaye ya kuma dawomin dakai lafiya"
"Ameen"nace kana na kashe wayar.
Har na fito daga gidan na tuna dacewa ashe ina da tsohon I. D card 'dina wanda ya 'bata kwanaki,ban ganshi ba sai bayan na kar'bi sabo a office wanda yanzu haka yana hannun Alh. Jaheed Auwal. Bayan na 'dauka ne naci gaba da tafiya zuwa tashar 'yankaba anan na iske mota mai zuwa Hadejia ta kusan cika mutum 'daya ake jira lokacinda na isa. Bamu isa ba sai misalin 'karfe hud'u da rabi na yamma. Wani 'dan acaba na samu nake tambayarsa "Malan dan Allah tambaya nake"
"Allah yasa na sani"
"Wani 'kauye nake tamabya Busuku"
"Busuku,kai! Amma a wanne local government 'din aka ce ma garin yake"
"Kirikasamma"
"Gaskiya ban san garin ba,amma sai dai ko idan kaje can kirikasamman ba zaka rasa wanda yasan garin ba"
"To kai ni man tashar da zata kaini kirikasamman"
Bayan ya saukeni na sallameshi,na zauna zaman jiran mota ta cika. Na jima a zaune ina jira ta cikan amma shiru babu alamar mutane masu zuwa garin. "Direba ya kamata mu tafi,dare yana gabato mu fa"nace dashi a lokacinda na kasa jure jiran
"Mu tafi ina,ai sai motannan ta cika kafin mu barnan. Idan kuma kana saurine zaka iya 'daukata shata"
"Kamar ya shata"
"Ina nufin ka biya ku'din sauran kujerun da ba fasinja"
Dolena na hakura na koma na zauna zaman jira har na tsawon wasu lokuta sannan mutum uku suka zo,saura mutum 'daya. Ba a jima ba 'dayan shima yazo,anan mukashishshiga bayan sun karbi 'ku'da'denmu muka fara tafiya.
Mintuna ashirin da fara tafiyarmu muka iso garin,a bakin titin garin na had'u da wasu 'yan mata guda uku 'daya tana tallan pure water,dayar kuma goro ne a kanta a yayinda 'dayar ke 'dauke da tire cike da rogo. Matsawa nayi kusa dasu bayan na musu sallama"'yan mata sannunku"
"Yauwa"suka amsa a tare
"Dan Allah tambaya nake"
"Allah yasa mun sani"
"Wani 'kauye Busuku nake tambaya"
"Eh mun sanshi amma 'kauye ne mota bata zuwa sai dai a babur"
"Nagode"nace dasu a lokacinda na 'dagawa wani 'dan acaba a hannu,ya iso gareni "nawa zan baka ka kaini Busuku yanzu"
Ka kawo 'dari hudu maigida"
"A'a zan baka jaka dai"
Dakyar muka daidaita a dari uku. Har cikin garin ya saukenibakin wani shago na 'kasa,sai dai lokacin ana kiran sallar Isha'I. Anan nima nayi alwala na rama sallolin da banyi ba a masallaci kusa da shagon. Sannan na fito daga masallacin na isa wajen mai shagon "Mal barka dai,don Allah ni ba'ko ne ina neman inda za'a taimakamin na kwanta zuwa gobe"
"Allah sarki! Insha Allah ba matsala zaka samu" yace dani
"Yauwa nagode"
"Babu komai. Akwai 'dakina ni ka'dai ne a ciki ya ishemu"
»». »». »»
Washe gari na nemi yamin iso wajen dagacin garin don ganawa dashi. Bayan munje ne na gabatar da akaina a matsayin ma'akacin kamfanin sadarwa na MTN. Sannan nazo ne neman wata Jamila Abubakar domin 'danka mata hakkinta na tallar kamfaninmu da tayi.
"Kai!Gaskiya a kaf garinnan babu wata mai irin wannan sunan"dagacin yace dani. Jotter na 'dauko wacce na rubuta tattaunawarmu da ita,sai a sannan na lura da cewa Abubakar 'din sunan mijintane da ya rasu. Amma ainahin sunanta Jamila Abdullahi Adamri kamar yadda ta fadamin.
"Jamila Abdullahi Adamri nake nufi"nace da dagacin
"Adamri?"
"Eh"
"Tabbas akwai Adamri a garinnan sai dai ya rasu"
"Amma bashi da 'da?"
"'dansa 'daya ne sunansa Auduwa"
"Ko zan iya samun sa?"
"Ai ya jima rabonsa da garinnan,tun wani sa'bani da suka samu da mahaifinnasa ya fita ya bar garin bai sake dawowa ba har yanzu shekaru talatin kenan".
"Yanzu duk wannan tafiyar da wahalar da na sha nayi ta yita a banza kenan"nace a raina lokacinda muka dawo gida daga wajen dagacin. Jotter na 'dauko na sake dubawa a karo na biyu ina nazarinta,sai a sannan na lura da sunan garin mijinta da ta fadamin a tattaunawarmu. "Dole tunda ban samu yadda nake so ba anan,naje can kila na dace da wani abu.
Washe gari da misalin karfe 09:00am na isa kakori garinsu Abubakar dake jahar yobe bayan doguwar tafiya cikin kwale-kwale. Anan bayan na sau'ka a jirgin na ha'du da wata mata mai 'dan jiki ka'dan,kallo 'daya zaka mata ka tabbatar da cewa ba bahaushiya bace saboda irin yadda aka tsatstsaga mata fuska wato 11 11. Matsawa nayi kusa da ita muka gaisa sannan nake tambayarta ko ta san wani Abubakar Garba.
"Eh nasan gidansu dai"tace dani,anan tamin kwatancen gida na kama hanya har kofar. A daidai kofar gidanne na ha'du da wani tsoho yana fi'ke 'kaho a jikin wani dutse dake 'kofar gidan. Kai tsaye na tunkareshi muka gaisa sannan na tambayeshi ko yasan Abubakar Garba. Sai da ya 'karemin kallo sannan yace dani "akan me kake nemansa" anan shima na 'kir'kiri wata 'karyar na kifar dashi. Gamsuwar da yayi da 'karyar da na shirgamar ce tasa ya bani damar na biyoshi izuwa cikin gidannasa domin tattaunawa.
Da'alama shi ka'daine a gidan domin dai har ya shigar dani ciki banga kowa ba, a cikin 'dakinsa muka zauna sannan ya fara magana "tabbas na san Abubakar Garba hasalima nine mahaifinsa, a lokacinda Abubakar yake tare dani na sha fama dashi akan 'kwace da cin zalin mutanen garinnan da yake. Ko ka'dan halinsa ba mai kyau bane,nayi 'ko'karin ganar dashi amma Allah bai nufa ba. Ya jawomin abubuwan kunya da dama a wannan 'kauyen namu,wannan dalilinne ta sani na tsine mar sannan na koreshi daga gidana"cike da 'bacin rai yakemin wannan batun
"Wato baba sau tari dama ana samun haka,sai kaga yaro ya taso da wasu munanan 'dabi'u amma cikin ikon Allah sai ya shiryeshi,da ace kaga irin matar da 'danka ya aura tabbas zakayi mamaki. Saboda babu ta yadda za'ayi mai hali irin wannan ya samu mallakar mace mai hankali,nutsuwada kyau irin ta ba. Don haka kada kayi mamaki idan nace ma 'danka ya canja daga halayensa munana da ka sanshi dasu da. Yaanzu tambayar da zan ma shine yaushe rabonka da Abubakar?"
"Rabona dashi tun shekaru shida da suka wuce,naji labarin yaje wajen 'dan uwansa babban 'dana dake kano. Nan shima na aika masa da ya koreshi a gunsa"
"Ko zaka iya fa'damin adireshin babban 'dannaka?"
"Eh". Anan ya fa'damin ni kuma na rubuta a jotter. Bayan na masa godiya na mi'ke domin komawa gida (kano).
Ban isa kano ba sai da daddare misalin 'karfe goma sha 'daya (11:00). Naso na 'danyi nazarin abubuwan da ya kamata nayi amma ban samu dama ba sakamakon matsananciyar gajiyar da ke damuna,bisa dole na shiga 'daki na kwanta. Ban farka ba sai da gari ya waye rana ta fito,bayan nayi sallah na shiga kitchen domin kimtsa kaina sannan na wuce ban'daki watsa ruwa. Bayan na gama shiryawane na fito domin zuwa gidan yayan Abubakar kamar yadda tsohon ya kwatantamin. Ban sha wahala ba wajen samun gidan,sai dai banyi sa'ar samun maigidan ba sai matarsa kawai na iske. "Sunana Haidar Ali,ni 'dan Jarida ne daga Mikiya"nace da ita a lokacinda nake nuna mata I.D card 'dina
"Lafiya?"
"Lafiya kawai inason ganawa da maigidanne akan matar kaninsa Jamila Abubakar"
"Sai kuma gashi maigidan baya nan,kumama ko yana nan banajin zai taimakama domin dai ya jima rabonsa da 'dan'uwannasa sann....."Bata 'karasa zancentaba wata mota ta 'karaso izuwa kofar gidan "shikenan ma ga yayannasa yazo"tace dani a lokacinda motar ta tsaya a kofar gidan!
Bayan mun gaisa na sake gabatar da kaina a wajensa,anan yamin iso izuwa cikin gidannasa. "Shekara shida kenan yanzu rabona da shi, waccan lokacinda yazo hannu bibbiyu na kar'beshi ina tunanin ko zai canja halayensa. Nayi 'ko'karin sama masa aiki a wani kamafanin da abokina ke aiki a matsayin masinja,amma munanan halayensa yasa suka koreshi. Nima da naga ba mai canjawa bane na sallameshi kamar yadda mahaifinmu ya umarcen. Amma nayi mamakin yadda kace ya canja har da matarsa"yace dani bayan mun zauna a 'dan madaidaicin falonnasae
"Hakane kasan komai mai iya canjawa ne,a wanne kamfani ne kace ka sama masa aiki?"
"Kamfanin takalma ne anan Jogana"
"Kace kuma shekaru shida da suka wuce ko?"
"Eh"
"Ko abokinnaka daya 'daukeshi aiki har yanzu yana aiki a kamfanin?"
"A'a baya nan"
"Nagode,insha Allah zanyi 'ko'kari naga na sameshi domin ha'duwa da matar"nace dashi a lokacinda na mike tsaye ina 'ko'karin fita.
Kai tsaye kamfani takalmin na wuce..
Sai kuma da daddare!!!