TSEGUMI-04
.
Da misalin sha biyun rana na isa gida (12:00am),sai a sannan na lura da matsananciyar yunwar da ke damuna,kasancewar rabona da abinci tun yammacin jiya. Kitchen na fara wucewa anan na ha'da shayi da madara na kurba kafin daga bisani na wuce office cike da fargabar abin da zai biyo baya idan na sanar da maigida abinda ya faru dani. Kai tsaye ofishinnamu na fara shiga
"Kai! Haidar me ya faru dakai,sai kace wanda ya shafe shekaru ba bacci"abokin aikina yace dani a lokacinda na shigo
"Hmm abubuwa dayawa sun faru"nace dashi a lokacinda nake 'ko'karin zama a kujerata kana 'dora da cewa "ina cikin ru'du da tashin hankali"na sanar dashi duk abubuwan da suka faru dani
'Kuramin ido kawai yayi sannan ya fara magana "amma ya zakayi,kasan fa Maigida bayason gardama gashi kuma ka bijire umarninsa"
"Na sani shi yasa ma nazo da shirina domin nasan bazai barni ba,amma dai sai na fa'damar duk abubuwanda suka faru"
"Me kuma kake 'ko'karin yi gameda barazanar da Jaheed Auwal yama,kasan fa masu kudinnan suna da damar yin duk yadda suka so a 'kasarnan"
"Hakane,kamar yadda na fa'adama babu wata hanya da wannan matar zata kasance matarsa kamar yadda yake so nayi saboda ba ita 'din bace. Amma dai akwai wani 'boyayyen al'amari game da ita. Gameda barazanarsa kuma,akwai hanyoyi biyu da na samarwa kaina. Na farko shine zanyi 'ko'karin neman mutane da zasu taimakamin su ro'kamin afuwarsa,ko kuma dai nasan yadda zanyi na bar 'kasar gabaki 'daya".
"Amma baka tunanin yanzu haka yasa yaransa suna kula da duk wani motsinka?"
"Komai zai iya kasancewa kam"nace dashi a lokacinda na mi'ke tsaye."Bari naje naga maigida (Ibrahim Atiku)".
Waya yake lokacinda na shiga ofishinnasa,saidai hakan bai hanashi zubamin na mujiya ba lokacin da shigo
"Haidar me ya faru dakai"yace dani bayan ya ajiyae wayar
Ban tsaya wata-wata ba nan shima na kwashe labarin abinda ya faru dani na fadamar
"Kana nufin kace sai da kaje gidan Jaheed Auwal duk kuwa da cewa na hanaka"
Shiru kawai nayi bance dashi 'kala ba,hakanne ta sa yaci gaba "ka jefa kanka a matsala Haidar,sai dai ina so ka sani nima bazan iya ci gaba da zama dakai ba anan saboda zaka iya jazamin. Alfarma 'daya da zan ma itace idan har ka tabbatar da aikinda ya sa kan cikin kwanakin da ya 'kayyade to zaka iya dawowa kaci gaba da aiki,amma yanzu kam na koreka"
.
Na fusata ainun da kalamansa domin dai bai min adalci ba musamman idan yayi la'akari da cewa na fa'da wannan 'kangin ne sanadiyyyar 'daga sunan ma'aikatar
"Amma idan akamin haka ba a min adalci ba"
"Haka kace? To tunda kana ganin ba'a ma adalci ba me zai hana kaje ka tabbatarwa da duniya cewa Jamila Abubakar itace Fatima Jaheed sai ka buga jaridar 'kar'kashin ikonka na tabbata wannan labarin zai 'daukaka tattalin arzi'kinka,har ka kafa taka ma'aikatar"
"Amma ku'din sallamata fa"
"Wanne sallama kuma,ka tunamin ma. Duk wasu abubuwa da kasan ma'aikatar nan ce ta baka to ka dawo dasu,sannan gameda motarka kuma za'a dawo maka da ku'da'denka da aka yanka,itama zaka ajiye mana ita.
"Ban ta'ba zaton zakamin haka ba Maigida"
"Zan iya ma fiye da haka ma Haidar,sannan ina so in sanar dakai cewa ko da Jaheed Auwal zai zo nan nemanka zamu fa'damar bamu ma sanka ba"
Da wannan na fice daga office 'din cike da takaici izuwa office 'dinmu.
"Ibrahim ina so zakamin wani taimako don Allah"nace dashi a lokacinda nake tattara kayayyaki na
"Kamar name fa?"
"So nake ka buga tattaunawar da mukayi da Jamila Abubakar a jaridar da zaka fitar na wannan makon"
"Insha Allah ba matsala,sannan ka 'dauki abubuwan da suka faru a matsayin 'kaddara insha Allah,Allah zai fidda kai"
"Babu komai Insha Allah zanyi 'ko'kari. Nagode"nace da shi,kana na fito daga office 'din kaina a sunkuye kamar wani mai nazarin 'kasa.
A gida cikin 'dakina tunanin abinda ya kamata na farane ya ziyarci kaina. "Gaskiya aikinnan da zanyi yana bukatar kudi nace a raina,hakanne ta sani fita izuwa banki domin duba ragowar kud'ad'en da suka ragemi a account 'dina. Duka-duka naira dubu ashirin ne sukai saura,sai a sannan na lura da wautata na yin facaka da kisan kwaf 'daya da nake wa kud'i a duk lokacinda na samesu. "Babu shakka ina bu'katar 'kudi ko dan tserewa na bar 'kasar a lokacinda naga ba haza". A hanyata ta dawowa daga bankin ina nazarin inda zan samu 'kud'I ko da aro ne domin fara bincike amma na rasa,sai daga baya na tuno da budurwata AISHA BELLO kasancewarta ma'aikaciya. Ko kad'an na'ki jinin kar'bar kud'I daga wajen mace musamman ma budurwa domin ina ganin hakan kwafsi ne da zubdawa kai kima,shi yasama kawai na yanke 'kudurin fara aikin da abinda ya ragemin kafin su 'kare.