Gaskiya Dokin Karfe

Galadima.com.ng Domin sharhi kan al amuran yau da kullum

TSEGUMI 03

TSEGUMI-03
.
"Ni dan jarida ne" dashi, a lokacinda nake 'kokarin fiddo da I.D card 'dina a aljihu. Tsawar da ya dakamin ce ta dakatar dani "kada ka sake ka motsa,idan har baka son yanzunnan na fatattaka 'kwa'kwalwarka da harsashi. A haka na tsayar da hannunnawa shi bai 'karasa aljihun ba sannan ban dawo dashi dai-dai ba.
"Menene sunanka?"Yace dani a karo na uku
"Sunana Haidar Ali "
"Me ya kawo ka gidana?"
"Labarin yana da tsa..."Tsawar da ya dakamin ce a karo na biyu ta katsar dani daga furucinda nake
"Kawai ka fadamin me ya kawo ka nan" da alama ya fara fusata,sai a sannan zuciyata ta fara tunano min da gargadin da maigidanmu yamin. "Babu shakka bani da wani bambamci da gawa"zuciyata tace dani,"amma zai iya ma rangwame idan har zaka fadamar ha'ki'kanin abinda ya kawo ka gidannasa" wata zuciyar tace dani
"Kwanaki hudu da suka wuce ne na ha'du da wata mata da tai matukara kama da wannan matar taka a kano. Hatta yanayin tafiya,murya da komai nata iri dayane da na wannan matartaka. Nayi 'ko'karin tambayarta ko su 'yan biyu ne amma sai tace min a'a. A yanayin yadda na lura da tsarintane zuciyata take rayamin cewa ba gaskiya take fa'dan ba a dalilin hakanne ma naje na binciko da tsohuwar jaridar da ta buga labarin mutuwar matarka domin tantance hoton. Anan ne mamakina ya 'karu saboda tsantsar kaman da sukayi,nayi 'ko'karin mantawa da batun amma zuciyata taci gaba da fisgata akan gano ha'ki'kanin gaskiya. Shine na yanke shawarar zuwa domin tabbatar da cewa ba ita 'din bace.
Har yanzu idanunsa 'kyar a kaina baya ko 'kiftawa a lokacinda nake magana sai dai ya canja saitin da yawa bindigar daga idona zuwa kirjina 'bangaren hagu."Kace yanayin tafiyarta ma 'daya ne da ta matata?"Yace dani
"Eh"
"Kasan matata ne lokacinda take da rai?"
"Eh na santa,domin na halarci 'daurin aurenku"
Sake kuramin ido yayi kafin daga bisani yace dani "ya sunan ita matar da ka gani?"
"Sunanta Jamila Abubakar"
"A ina take da zama"
"Ban sani ba"
"Aikin me take?"
"Ina tunanin ma'aikaciyar banki ce amma banajin 'yar kano ce"nai masa 'karyane saboda gudun kar yabi sawunta domin yanzu kam na tabbata waccan din ba matarsa bace
"A wanne ma'aikatar jaridar kake aiki?"
"Mikiya"
"Nuna min I.D card 'dinka"
Naji 'da'din hakan domin samun hutun da hannuna yayi daga gajiyar da yayi,tuni ya fara 'kagewa
"Shillo min"yace dani bayan na dauko.
"Juya bayanka ka kalli bango"yace dani a lokacin da yake 'ko'karin sunkuyawa ya 'dauka.
Bayan kamar da'ki'ka uku yana nazarin I.D card din ne ya sake cewa dani "garomin da kamerarka"
"Tsaya yadda kake"yace dani sannan ya dau'ken kamerar,"matso ka dafa gawar" sannan ya sake 'daukata
"Taya akai ka shigo nan?"
Bayan na fadamar ne ya umarceni dana bashi duk kayayyakin da nayi amfani dasu wajen shigowa.
"Ka saurareni dakyau"yace dani "na baka nan da kwanaki goma sha hu'du (sati biyu)ka tabbatar wa da duniya cewa matar da ka gani itace matata da aka kashe"
"Amma taya?"Nace dashi
"Kai ka sani,ni dai burina kenan. Idan kuwa ba haka ba rayuwarka tana cikin garari domin baka da bambanci da gawa"yace dani sannan ya umarceni dana fito waje a hankali har zuwa farfajiyar gidan. Anan ya kira maigadin gidan ya rakani waje.
.
Washe gari a hanyata ta dawowa gida zuciyata taci gaba da sake-saken da nasan ba fiddani zasuyi ba,babu ta yadda za'ai na tabbar wa da duniya cewa Jamila Abubakar itace Fatima Jaheed domin kuwa ko ni kaina nasan ba hakan bane. Sai dai har yanzu akwai wani abu da nake ji a jikina dake nusar dani hakan mai yiwuwa ne,babu shakka akwai wani abu 'boyayye game da Jamila Abubakar amma zuciyata ta gaza gano menene. Tunanin gano 'boyayyen al'amarinne ya fara zarya a 'kwa'kwalwata amma na rasa ta inda zan fara,"hava sai kace ba 'dan jarida ba"zuciyata tace dani. Tunanin wasu kyaututtuka da aka baiwa wasu 'yan jaridu shekarar da ta wuce saboda 'kwazonsu ne ya fa'do zuciyata,a waccan lokacin ina daga gefe ina kallon yadda ake kiran sunansu 'daya bayan 'daya ana dan'ka musu kyaututtukan. "Babu shakka zan jarraba ko dan NEMAN SUNA da kafa tarihi a duniyar binceke"da irin wa'dannan sa'ke-sa'ken na iso gida KANO.