TSEGUMI-02
.
Na tsorata matuka da yadda ta nuna tsantsar fusatarta akan daukanta danayi a hoto a lokacinda ta shigo,anan ta bukaci na bata film din dake ciki amma sai na mata karyar cewa na daddauki abubuwa dayawa a cikinsa kuma idan har na zaro yanzu to zanyi asarar komai. Bayan ta gamsu da batuna ne ta gargadeni akan kada na kuskura na dora hotonta akan labarin da zan buga,sannan ta umarceni da na kawo mata negative din hoton washegari. Anan muka ci gaba da tattaunawa amma ba kamar da ba
A hanyata ta dawowa gidane nake ta sake-saken abubuwan da suka wakana tsakanina da ita "Me yasa ta fusata don kawai na dauketa a hoto? Me yasa bata son a buga hotonta a jarida? Me yasa ta bukaci nakawo mata negative din hoton?
"Babu shakka sai na wanke hoton kafin na kai mata negative din,saboda anan ne zan bambanceta da Fatima Jaheed dake jikin jarida"nace a raina. Kai tsaye gidan wankin hotunan na wuce sannan na dawo office domin ci gaba da bincike.
.
Sosai basu da wani bambamci da juna,ko makaho zai tabbatar da haka idan ya shafa hotunan.
Wani tunanine ya darsu a zuciyata a lokacin da nake duban hotunan "kodai 'yan biyu ne"na tambayi kaina. Kwata-kwata bani da niyyar maida mata da negative din amma da wannan tunanin yazominne naga dacewar hakan domin tananne zan samu damar tambayarta ko su 'yan biyu ne.
Washe gari da misalin karfe goma sha daya na safe (11:00am) bayan na fito daga ofishinmu na wuce kaina tsaye zuwa Khairat night Club. Nayi mamakin yadda masu gadin suka tarbeni "ka shiga ciki Hajiya tana jiranka" suka ce dani sabanin jiya da sai da akamin iso. Kai na tsaye na wuce har ciki,anan ne na hadu da matar da ta shigar dani jiya. Bayan mun gaisa ne take cemin "ka zauna anan,zanje na fadamata ka iso daman kai take jira" tace dani a lokacinda ta nuna min kujera kana ta wuce izuwa ofishin Hajiyar.
"Ina negative din"tace dani a lokacinda ta shigo bata jira mun gaisa bama
"Gashinan"nace da ita a lokacinda na mika mata envelope din da na saka negative din. Sai da saitashi da hasken kwan lantarki domin tabbatar da cewa shi dinne sannan ta dubeni a karo na biyu tace dani "ka tabbata baka wanke hoto ko daya ba"
"Ban wanke ba" nace da ita cike da karfin gwiwa. Bata ce dani kala ba saima juyawa da tayi izuwa inda ta fito
"Hajiya ko ke 'yan biyu ce"nace da ita a lokacinda take kokarin fita. A gaggauce ta juyo cike da mamaki. Wani murmushi ta harbeni dashi mai kashe zuciya sannan tace "Me yasa mutane da dama sukemin wannan tambayar,nayi kama da wata wacce ka sani ne"
"A'a haka kawai nake ji a jikina"nace da ita
"Amma taya zakaji hakan a jikinka"
"Wato baki gane bane,kinsan mu 'yan jarida wasu lokuta mukan bijirowa da mutum da wasu tambayoyi wanda zaki dauke su marasa ma'ana da kan gado don samun karin bayani,saboda wasu amsoshin sai a irin wadannan tambayoyin muke samu"nace da ita
Da'alama ta gamsu da abinda na fadamata "a'a ni kadaice,bani da kanwa,kani ko yaya,ni kadai iyayena suka mallaka"
.
Lissafina ya sake birkicewa ina ta sake-sake a zuciyata lokacinda na isa ofishinmu "da ace tacemin ita 'yan biyu ce to da shikenan zan dauka cewa Fatima Jaheed 'yar uwarta ce amma ita kadai ce". Hanya dayace da zan bi na gano ainahin wannan rikitaccen al'amari,shine zuwa gidan Jaheed Auwal domin ganin gawar Fatima Jaheed.
" ko kadan kada kayi gangancin zuwa gidansa da niyyar wani bincike a kanta,zai iya hallakaka domin tuni ya fara nisa a duniyar mahaukata saboda tsabar so" gargadin da maigidanmu yamin ne suka fara zarya a kwakwalwata
Kintacen irin abubuwan da zasu faru danine idan Alh.Jaheed Auwal ya kamani a gidansa suka fara zarya a kwakwalwata. "Tabbas zai iya harbeni a matsayin dan fashi musamman idan akayi sa'a yana da bindiga,ko kuma yasa a tsareni bakin rayuwata domin yana da damar yin hakan musamman a halinda kasarnan tamu ke ciki" wata zuciyar kuma cewa tayi dani "baka da wata hujja da zaka kare kanka a ko inane idan har ya kama kan,zai iya huce haushin cin amanar da masu kisanta suka mar a kanka idan ma bai daukeka a matsayin daya daga cikinsu ba" girgiza kai nayi cike da karaya,tuni na fara yanke shawarar fasa zuwa gidan don ganin gawar
"Ai kuwa idan banje ba,babu ta yadda za'ai na warware wannan sarkakiyar,kuma ma ina amfanin karatunda nayi idan har bazan iya warware wannan ba" da irin wadannan shawarwari da zuciyata ke rudata akai ne na yanke kudurin zuwa gidan.
Washe gari a office ina zaune ina aiki,a yayinda shi kuma Ibrahim na nasa aikin a daya gefen. Maigidanmu ya shigo (Ibrahim Atiku) "Haidar ina son ganinka yanzu a office"yace dani. "To yallabai"nace dashi sannan muka gaisa ya koma izuwa ofishin nasa. Bayan na kammala abubuwan da nake ne na iskeshi a ofishin nasa
"Haidar inaso zan saka wani aiki wanda a kalla zai daukeka tsawon wannan ranar"yace dani
"Yallabai wallahi bazan samu dama ba,ina so yau zanje kaduna ne"nace dashi
"Kaduna?"
"Eh"
"Me zakayi a kaduna?"
"Abokina ne yake fama da matsananciyar jinya,sannan yana bukatar taimakona. Ya taimakamin matuka a lokacinda nake karatu"
"Aikin yana da matukar muhimmanci"yacedani
"Yallabai wallahi bazan samu dama ba saboda tamkar dan'uwa yake a wurina. Sai dai ko amin uzuri zuwa gobe idan na dawo"
Zubamin ido kawai yayi a lokacinda nake masa bayanin,nasan tuni ya fara kufula dani
"Ina fatan dai ba gidan Alh. Jaheed zaka ba"yace dani
"A'a yallabai"
"Ko da wasa kada kuskura kaje nan"
"To yallabai" nace dashi kana na fito daga ofishin
Kamar yadda na tsara da misalin karfe biyar na yamma nake son kama hanya saboda isa garin da daddare. Sai da na fara biyawa kasuwa na sayi duk wasu abubuwa da zan bukata wajen shiga gidan sannan na samu wuri nayi fakin din motar ina jiran lokaci. Da misalin karfe daya da rabi na dare ne na iso kofar gidan (01:30am) babu wani abu daya canja na daga tsarin gidan kamar yadda yake da shekaru uku baya da suka shude. Da taimakon igiyar da na siyo ne na samu damar haura katangar gidan, a hankali na fara waigen ko ina na tsakar gidan ko da wani yaji motsina lokacinda nake haurowa.
Sai da na gama nazarin gidan daga inda nake rakabe a jikin bango!a hankali na fara tafiya cikin sanda izuwa bakin kofar gidan. Ban sha wahala ba wajen bude kofar duk kuwa da cewa bana tare da dan makullin gidan da taimakon wasu 'yan kananun wayoyi da nayi amfani dasu. A cikine idona suka fara tsintar haske daga wasu dakuna a hawa na sama na cikin gidan,cikin sanda da taka tsan-tsan na hau saman benen a nanne na dan tsaya kasa kunne ko zanjiyo wani motsi daga ciki amma shiru.
.
A hankali na isa bakin kofar dakin da na hango hasken,na murda da niyyar budewa cikin sa'a kuwa ta bude. Lekawa na fara yi anan ne hangi tangamemen gilas lullube da kyawawan furanni,"babu shakka nanne dakinda ya ajiye gawar"nace a raina a lokacinda na shigo cikin da kin ina kokarin maida kofar na rufe.
Da gaggawa na matsa jikin gilas din na leka cikinsa,anan muka hada ido da ita. Mamakina ya karu a lokacin da nayi arba da kyakkyawar fuskarta,na kare mata kallo daga fuska har zuwa tafin sawu amma ban ga inda tayi bambanci da Jamila Abubakar ba. "To ko dai 'yan uku ne"zuciyata tace dani "To amma idan 'yan uku ne me yasa Jamila bata fadamin ba"wata zuciyar tace dani.
Tunanin daukar hoton gawar ne yazomin,anan na bude gilas din ina kokarin dauko camera tane naji motsin mutum a bayana. A firgice na juya.
Numfashina ne ya 'kage zuciyata ta dakata da bugun da take a lokacinda idanuna sukai arba da Jaheed Auwal jingine a bakin kofa rike da bindiga a hannu ya kuramin ido.
'Kura min idanun da yayi ne da 'yan mitsi-mitsin idanunsa masu kama dana maciji zuciyata ta tabbatar min da cewa ba zai min rangwame ba. Sai da ya gyara tsayuwa sannan ya saita 'yar karamar bindigar tasa saitin idona na dama kafin ya fara magana da wata kakkausar murya "WAYE KAI ?