TSEGUMINA-01
.
FARKO
Na shafe sama da shekaru biyu da 'yan watanni da kammala karatuna a jami'ar Ahmadu Bello dake garin Zaria ina ta buge-buge da fafitikar neman aiki. Kafin daga bisani na samu a daya daga cikin ma'aikatun Jaridun dake birnin dabo (kano) mai taken MIKIYA La'akari da adadin yawan ma'aikatantane zai tabbatar maka da cewa har yanzu da sauranta duka-duka bamu haura goma ba. Ibrahim Atiku shine mamallakin gidan jaridar mutum ne mai tsatstsauran ra'ayi girman kai ga saurin fushi. Kamar yadda yasha fadama mana "babu wani abu dayakai kudi muhimmanci a wannan rayuwar don haka dole ku bazama neman labarai wanda zasuja hankalin jama'a domin habaka asusun wannan ma'aikata da kuma dauwama akarkashinta" kalamansa ne suka shigo da gasa a tsakaninmu ma'aikatan kowa burinsa ya gabatar da labarinda zai ja hankalin makaranta. Wannan dalilin ne ya sani kai ziyara gidan shakatwa mai suna Khairat Night Club ko Allah zaisa nayi gam da katar da abin rubutawa. Bayan na biya kudin shiga ne na wuce kaina tsaye ciki, anan wani matashi ya tarbeni cike da fara'a yana cewa "yallabai barka da zuwa" ban amsa masa ba, burina na samu gurbinda zan zauna domin nazartar wurin. Kamar yasan abinda nake nazari "yallabai ga wurin zama yace dani a karo na biyu. Murmushi kawai nayi a lokacin da na kai dubana wajen da ya nuna min. Tabir ne a tsakiya da kujeru uku gewaye. "Nagode nace dashi a lokacinda nake kokarin zama a daya daga cikin kujerun. "Yallabai me za'a kawoma" yace dani "Me dame kuke dashi"nace dashi "Babu abinda bamu dashi yallabai na kayan shaye-shaye na daga lemuka kai har da giya ma idan kana bukata" "Hmm ni din dai Maltina nake da bukata" Dakikai biyar da kammala shan lemonne na fara nazartar yanayin wajen a hankali daga wannan sashe zuwa wannan. Babu shakka wurin ya hadu, sauran mutane da ke ciki na harkar gabansu a yayinda wasu ke ta faman tikar rawa kamar wasu 'yan mazari. Nayi kokarin gano inda sautin kidan ke tashi amma na kasa. Tunanina ya katse ne a daidai lokacinda idanuna sukayi arba da wata kyakkyawar budurwa tana shigowa. Karuwar da kyanta ke yi ne a daidai lokacinda take kusantata yasa zuciyata tabbatarmin da cewa aljanace. Cikin wani salo ta dubeni cike da murmushi hade da kada 'yan yatsunta a sama ta wuce ta kusa dani. Sai dai wani abu daya dauremin kai bayan kyawun surarta shine irin yadda nakeji a jikina kamar mun taba haduwa, sai dai na kasa tunano inda na santa. Hannu na dagawa matashin daya fara tarbata, a gaggauce ya iso gareni. "Wacece wannan matar data wuce yanzu nace dashi "Kana nufin Hajiya, ai itace mai wannan gidan yace dani "Ina tayi" "Ta wuce office "yace dani a lokacinda yake karemin kallo daga sama zuwa kasa, babu shakka ya raina matsayi da shigata. Naso na samu ganawa da ita amma sai wani bangare na zuciyata ke shawartata akan mai zai hana na fara gano inda na santa tukun kafin na tunkareta. Da wannan tunanin na fito daga gidan shakatawar izuwa inda na ajiye motata da niyyar komawa gida a zuciyata ina ta nazarin wajenda na santa amma shiru.
.
A daidai lokacinda zan shiga gidane zuciyata ta daukomin hoton inda muka hadu. Babu shakka itace wacce Abokina ya taba gayyata ta daurin aurenta da kawunsa Alh. Jaheed Auwal a garin gwamna (kaduna) shekaru uku da suka wuce. Zuciyata taci gaba da daukomin hoton wurare da mutanen da suka halarci bikin kallo daya zakawa Ango da Amaryar zaka tabbatar da cewa aure ne na kudi ba wai soyayya ba domin duk inda mummuna yakai to Alh. Jaheed Auwal ya wuce nan. Kakkaurane baki mai faffadan baki bajajjen hancinsa ne zai hanaka yin tozali da mitsi-mitsin idanunsa masu kama da na maciji. "Babu shakka itace ,amma ai ita an kashe ta. hakanaci gaba da kasancewa cikin rudu da tunani.
Washegari da safe bayan na tashi daga bacci ina shirye-shiryen tafiya wajen aikine zuciyata ta sake bijiro min da tunanin matar da na gani daren jiya, naso na kawar da tunanin daga kaina amma na kasa "mai zai hana ka kira Maigidanku ka sanar dashi game da haka babu shakka bazaka rasa kofin jaridar da ta sanar da mutuwarta ba" da wannan tunanin na dauko wayata na danna lambobin Maigidan namu Ibrahim Atiku. Bayan wasu sakanni aka sadani dashi
"Hello Haidar aka amsa a daya bangaren
"Yallabai barka da safiya nace dashi
"Yallabai dama na kirane akan wata muhimmiyar magana da nake so zamuyi"
"Ina jinka"
"Daren jiya ne na kai ziyara Khairat Night Club...."
"Dafatan dai ka samo mana labari" ya katseni
"Eh to ba sosai ba, amma dai na hadu da wata mata wacce tayi matukar kama da Fatima Jaheed ko zaka iya tuna wannan sunan"nace dashi
"Kwarai kuwa itace matar Jaheed Auwal wacce aka sace sannan aka bukaci naira miliyan goma matsayin kudin fansa amma suka kasheta bayan ya biya kudaden"
.
"Yauwa,kamar yadda na fadama jiya na hadu da wata da tayi tsananin kama da ita sannan itace ma mai gidan shakatawar, sai dai ban mata magana ba. Zuciyata tana tabbatar min da cewa lallai itace matar Jaheed Auwal"
Dariyar da yake yine ta matukar bata min rai, sai da yayi ya gaji ne sannan ya fara magana "Wato Haidar da'ace daren jiyane ka kirani kake min wannan zancen to zan dauka cewa ko kana cikin maye ne"
"Yallabai kar kamin gurguwar fahimta mana
nace dashi a fusace "Na dauka cewa kayi matar da ka gani itace Fatima Jaheed"
"A'a nace dai tayi matukar kama da ita"
"Ok na gane kuma". Ya dan tsagaita kafin ya dora da cewa"babu ta inda zai yiwu ace matar da ka gani zata iya zama Fatima Jaheed domin a halinda ake ciki yanzu mijinta Jaheed Auwal ya adana gawarta a cikin gidansa bai bari an binne ta ba saboda tsantsar kaunarta da yake. Kamar yadda 'yan jita-jita ke ta yadawa a kowanne wayewar gari yana zuwa wajen gawar sau uku dauke da kwanon abinci wai ko zata farka. Don haka ka cire tunanin cewa matar da ka gani zata iya kasancewa ita"
Kamar ya san abinda nake tunani ya kara da cewa " ko kadan kada kayi gangancin zuwa gidansa da niyyar wani bincike a kanta, zai iya hallaka ka domin tuni ya fara nisa a duniyar mahaukata saboda tsabar SO
.
Mu biyu ne muke aiki a dan madaidaicin office din da aka tanadar mana nida abokin aikina Ibrahim. Sai dai yau ban samu zama a office din ba sakamakon binciken jaridar da ta watsa labarin mutuwar Fatima Jaheed a store da nake, na jima ina bincike kafin daga bisani na samu ciki kuwa harda hoton marigayiyar da sauran bayanai gameda mutuwar tata. A office ne na danyi nazarin jaridar na 'yan wasu lokuta sannan na dago da kaina na dubi Ibrahim nace dashi "Ina so yau zanje khairat Night Club don ganawa da mai club din" "Amma akan me"yace dani "Neman labarai"
.
Da misalin karfe goma da rabi na safe (10:30am) ne na isa wurin. Cikin uniform wasu mutane biyu ne jiki an rubuta Khairat security da alama sune masu gadin wurin. Kai tsaye na isa wajen su "Barkanku dai nace dasu
"Yauwa barka dai"suka amsa a tare
"Sunana Haidar Ali, ni dan jarida ne daga Mikiya "Ko me kake bukata daga garemu"daya daga cikinsu yace dani
"Inaso ne zan gana da mai wannan gidan, musamman akan irin fice da club din yayi a wannan gari"
"Kayi sa'a kuwa yanzu Hajiyan Tazo, bari na sanar da ita"
Bayan kamar minti biyar da shigarsa ne ya fito "Madam zata ganka "yace dani
"Nagode nace dashi a lokacinda nake kokarin wucewa ciki "Dakata za'a zo a tafi dakai yace dani
Na jima a tsaye kafin daga bisani wata budurwa da akalla zata haura shekara ashirin ta iso garemu "wannanne yake son ganawa da Hajiya? tace da maigadin da yamin iso a lokacinda take nunani da dan yatsa
"Eh shine"
"To bismillah" tace dani
A ciki ne ta zaunar dani a cikin wani daki, da'alama an tanada shine domin tarbar baki. "Ka jira anan,Hajiya zata fito ku gana"tace dani kana ta fice daga dakin. Bayan kamar dakika goma aka bude kofar. A daidai lokacin da muka hada ido ne zuciyata ta kara tabbatar min da cewa lallai itace (Fatima Jaheed)
"Barka da safiya hajiya"nace da ita cike da girmamawa a lokacinda na mike tsaye
"Yauwa, zauna man"tace dani
"Sunana Haidar Ali daga MIKIYA"
"Kace kana son ganawa dani"
"Eh"
"Menene kake son sani game dani"
"Eh to na farko zanso na san sunan ki, ko kece mamallakiyar wannan gidan. Idan kece, taya akai kika mallakeshi? Wadanne irin matsaloli kika fuskanta yayin mallakarsa? Wadanne kwarin gwiwa kika samu? Menene kika sa a gaba? Me da me kika fi so? Menene kuma bakya so? Kina da aure? Wanne shawara zaki bawa masu son kafa kasuwanci irin naki?
Wani dogon ajiyar zuciya taja sannan ta dora da cewa "lallai zamu jima muna wannan tattaunawar, amma bari mu fara kada mu bata lokaci"
"Menene wannan tace dani a lokacin da na dauko 'yar karamar rediyo domin daukan bayanai
"Rekoda ce, saboda ba lallai ne na iya rubuta dukkan abinda zaki fada ba. Da taimakontane zan iya fitar da hakikanin abubuwan da zaki fadamin domi gudun kuskure a yayin bugawa nace da ita. Kada kanta kawai tayi alamar ta gamsu sannan ta fara sunana JAMILA ABUBAKAR ina da miji wanda ya mutu sanadiyyar hatsarin da sukayi a jirgin ruwa a hanyarsa ta zuwa garin iyayensa. Sannan na mallaki wannan gidane daga cikin dukiyar da mijina ya bari..
"Bayan wannan ko akwai wani abu da kika mallaka daga gareshi" na katseta
"Akwai gida wanda nake cikinsa da sauran ababen hawa"
"Amma shi mijin naki bashi da 'yan uwa ne ko iyaye"
"Akwai amma ban sansu ba, hasalima babu wani daga danginsa daya halarci daurin aurenmu.
"Amma taya akai kika ji labarin mutuwar mijin naki"
"Najine a kafafen yada labarai na gidan rediyo cewa jirgin da ya dauko fasinjoji daga kano zuwa yobe ya nutse a cikin ruwa. Bayan na jira banga dawowar maigidana ba ne naje ofishin 'yan sanda na sanar dasu, anan ne suka tabbatar min da cewa mijina yana daga cikin wadanda suka mutu"
"Amma kina tunanin kara aure"
"Har yanzu ban gama jimamin rashin mijina da nayi ba, amma da zarar naji saukin abin zan iya yin wani auren"
"Sai kuma ki fadamin abubuwan da kike sha'awa"
"Noma"
Ko kadan ban yarda da abinda ta fada ba. A lokacinne na duba agogon hannuna sai a sannan na lura da jimawar da mukayi a kalla mun shafe sama da awa biyu muna tattaunawa.
"Ina zuwa"tace dani a lokacin da ta mike
Wani tunanine ya bijiro zuciyata a lokacin da ta fita" ya kamata ka dauki hotonta yadda zaka kamantasu da waccan na jaridar". "Ba lallai ne ta yadda ka dauki hotonta ba" wata zuciyar tace dani. Yar karamar camera na dauko na saitata daidai bakin kofar da zata shigo yadda da zarar ta shigo zan dauki hotonta
