Assalamu alaikum
Yau za mu yi magana a kan yadda ake dawo da account din da aka yi disable. sai a biyo mu.
Abin da Ya kamata Ka Lura:
1. Ka karanta abin da facebook suka fada maka:
Sau tari idan mutum ya yi login bai bude ba ga bayani an rubuta amma ba zai karanta ba kawai sai ya ce wai an yi masa hacking.
Alamomin Da ke Nuna Anyi Disable Account Din Mutum :
1. Wasu za su ga an rubuta musu “Your account was disabled because we could not verify your account information. Learn about what we do and don’t allow by reviewing the Facebook Community Standards.
If you believe your account was disabled in error, please (let us know)”
2. Your account has disable. If you have any questions or concerns, you can visit our Help Center. CANCEL/OK
Wannan yawanci ga masu amfani da app ne.
3. Your account has been disabled. If you have any questions or concerns, you can visit our FAQ at https://fb.me.disabled
Wannan kuma a messenger.
Yadda Za Ka Dawo Da Disabled Account Din:
Yadda za ka yi shi ne idan na farko ne sai ka shiga “let us know” bayan ka shiga za ka cike form kamar haka:
1. Email/lambar wayar account din naka.
2. Cikakken sunan ka na facebook din.
3. Identity Card dinka, ko Voters card, Driving License, International Passport, Work ID Card da makamantansu. (wani za a ce sai ya tura guda 3 zuwa sama, wani kuma 1 kawai zai saka)
Idan an ce ka saka sama da hoto daya kuma wurin saka hoto daya suke bayarwa zaka tura sai ka kara tura sauran daya bayan daya.
4. Za ka rubuta karin bayani a kan ka cikin Harshen Turanci.
4. Sai ka danna Send/Submit
Domin cike wannan form kai tsaye ko cikewa wani sai ka bi ta wannan link din: https://web.facebook.com/help/contact/260749603972907?_rdc=1&_rdr
Amma sai ka yi log out din account dinka.
Zan dakata a nan sai a rubutu na gaba.