Yadda Zaka Gano Asalin Wanda Ya Fara Dora Wani Hoto A Internet
Assalamu alaikum, a yau zamuyi magana akan Google Reverse da kuma yadda ake amfani dashi, sai a biyomu.
Menene Google Reverse?
Google reverse tsari ne da google zai baka damar gano Ire-iren hotuna masu kamanceceniya da juna, da kuma bayanansu.
Misali ina da wani hoto sai nake so na samo Ire-iren sa to zan saka shi a Google Reverse su kuma zasu bani Ire-iren hoton dake internet, Sannan zasu bani bayanin wanda ya dora hoton da kuma kwanan wata da aka dora kowanne daga ciki ta nan zaka gano wannene aka fara dorawa.
‘Yan Jaridu a duniya sune kan gaba wajen yin amfani da wannan bangare kuma yana basu gagarumar gudummuwa wajen aikinsu.
Yadda Ake Amfani Da Google Reverse
Kamar yadda mukayi bayanin Google Image Search a baya shima wannan hakane zaka shiga kayi uploading din hoto shikenan zai kawo maka bayanansa, sai dai shi baya aiki a wayoyi sai dai a computer.
Amman a yanzu akwai shafuka da dama da aka samar a yanar gizo wadanda suke wannan aikin kuma suke bada dama ta gabaki daya mai waya da mai computer duka zasu iya amfani dashi ga kuma daya daga ciki:
https://www.labnol.org/internet/mobile-reverse-image-search/29014/
Zaka iya amfani da Google Search link https://images.google.com
Sannan zaka iya danne kan duk wani hoto daka gani a internet zai baka zabi aciki akwai “search google for this image” sai ka danna.
Zan dakata anan sai a rubutu na gaba.
Domin samun sauran rubutuka masu alaka da suka gabata sai a ziyarci www.sharfadi.com
Yanda Zaka Gano Wanda ya fara saka hoto a internet
Tags
# Fasaha
About Jamilu Ismail Muhammad
Soratemplates is a blogger resources site is a provider of high quality blogger template with premium looking layout and robust design. The main mission of templatesyard is to provide the best quality blogger templates.
Fasaha
Category:
Fasaha