- ATM kati ne da zai bawa mutum wanda yake da asusu banki damar cirar kudin sa a duk lokacinda yake so a kuma duk inda yake, wannan katin zai baka damar da wanda yake da asusun banki damar ciran kudi (wato kudin sa) a duk sanda yake so a kuma duk inda yake, Wannan kati zai maka dama ka ciri kudi maimakon sai kaje banki kabi layi ka cika teller, zaka iya cirar kudin ka ta hanyar amfani da wannan katin da sauransu.
- Katin atm kayi da da kusan zaace makulli ne na account dinka na banki, dashi zaka dinga amfani ko nawa kake dashi kaje ka cira.
- Sai dai shi wannaj katin iri-iri ne, kuma abubuwanda akeyi dashi daban-daban ne, katin ATM bayaga cirar kudi, ana iya sayayyar abu ta hanyar internet wato cinikin abu bayan ka saka wasu lambobi sai a ciri kudin, sannan ana iya sayayya a manya shaguna ko kamfanoni da sauransu da wannan ATM, ta yadda idan kayi sayayya zaka bayar ayi amfani da shi ATM za'a sashi a wani abu da ake kira da POS domin a cire wannan kudin,
- Dalibai na iya amfani dashi a makaranta wajen tura kudin makaranta da sauransu, amfani da remita anayin amfani da katin ATM.
- Saidai ATM dinnan kamar yadda na fada iri-iri ne, akwai wanda iya abinda zai iya maka shine ka ciri kudi a ATM MACHINE bayan wannan bazai iya maka wani abu ba. Sannan idan muka dauki VERVE samfuri ne irin na ATM amma shi abubuwanda yake iya yi shine zaka ciri kudi, baza ka iya biyan wani abu online ba da makamantansu.
- Kamar yadda ATM dinka zaka iya zuwa kayi amfani da ATM MACHINE ma'ana wuraren da aka yi su na cirar kudi da katin ATM zaka saka atm card dinka, idan ka saka zaka iya yiwa wani transfer, ma'ana akan ka ciri kudin cash a hannunka, zaka iya yin wannan, sannan abubuwanda zaka iya yi da katin ATM bayan wannan to zaka iya duba balance dinka, nawa ne ke cikin account dinka, to zaka iya amfani da shi ATM dinka.
- Shi wannan ATM CARD din akwai charges da akeyi a kanshi
- Duk wanda yake da ATM zaiga duk wata kamfanin waya suna tura masa da suna cirar kudi domin lura da suke yi masa da wannan katin.
- To wannan charging, amma abune da bai taka kara-ya-karya ba tunda abu ne dan kalilan, zaka iya amfani da ATM sama da guda daya
- Idan yanzu ina amfani da account na wani banki sai nake da ATM na VERVE to zan iya zuwa ayimin VISA ko MASTER CARD akan wannan account din guda daya? Eh kana yancin kayi amfani da ATM sama da guda daya, bayan wannan zaka iya amfani da ATM dinka ko da a bankin da ba naka ba, sau tari zaka ga mutum ya shi sai a bankin sa zai ciri kudi, ATM ba sai lallai a bankin ka zaka ciri kudi ba, a'a zaka iya amfani da bankin da ba naka bane ba kaje kasa ATM dinka kuma zai baka kudi, da yawa akwai mutanen da basu fahimci wannan ba, zaka ga suna shan wahala wajen cirar kudi saboda wannan matsalar,
- Katin ATM dinnan kamar yadda mutane zasu kare kansu daga samun matsala, daga cikin matsalolin da ake samu wajen amfani da katin ATM shine, mu anan sau tari zaka ga mutum yaje shi cirar kudi sai yace nashi yaki amma bari nayi maka transfer sai ka cirar mini, irin wannan matsalar ana samun shi da yawa, kuma karshe zaka ga an cuci wani, to wannan duka ya kamata mutum ya kiyaye in bai san mutum ba kada ya shiga irin wannan tsabgar, shima dau'i ne wasu ke amfani dashi don su cutar da mutum ta ATM, da mutum yayi maka transfer zai karbi ATM dinka ya cire kudin sa, wani kuma dama bai tura maka komai ba kawai don fraud ne yayi.
Hanyoyin da zakabi dan Kare ATM CARD dinka 001
Tags
# Fasaha
About Jamilu Ismail Muhammad
Soratemplates is a blogger resources site is a provider of high quality blogger template with premium looking layout and robust design. The main mission of templatesyard is to provide the best quality blogger templates.
Fasaha
Category:
Fasaha