Gaskiya Dokin Karfe

Galadima.com.ng Domin sharhi kan al amuran yau da kullum

ZA A GINA JAMI'AR MUSULUNCI A KANO

ZA'A GINA JAMI'AR MUSULUNCI A JAHAR KANO
Gani Ya Kori Ji Gashi Nan Ku Karanta
Muna Maraba Da Lale Da Sheik Dr.Pakistan A Cikin Katafaran Filin Da Mai Girma Gomnan Jahar Kano ( Khadimul Islam ) Dr.Abdullahi Umar Ganduje Ya Mallakawa Ahlussunnah A Kano Domin Su Gina Jami'a
Ganduje Ya Mallakawa Ahlussunnah Katafaran Fili , Girman Filin Hectar Dari ( 100 ) Domin A Gina Jami'ar Musulunci Ta Ahlussunnah
A Cikin Karamar Hukumar Kura , Kan Haryar Zuwa Zaria Filin Yake
Dr.Pakistan Yana Gayyatar Kowa Da Kowa Ranar 18-1-2019 A Rannan Ne Za'a Fara Saka Harsashin Ginin Wannan Jami'ar , kuma Mai Girma Gomna Da Kansa Shine Zai Jagoranci Saka Harsashin Wannan Ginin Da Kansa A Wannan Ranar
Mai Girma Gomna Ya Mallakawa Ahlussunnah Wannan Katafaran Filin Domin Gina Jami'a Ta Musulunci
Da Akwai Wasu Bayin Allah Da Zasu Tallafa Wajan Ginin Wannan Jami'ar Ta Musulunci Ta Ahlussunnah
Muna Addu'a Allah Ya Sakawa Kowa Da Al'kairi